Kamfanin Twitter Ya Rufe Shafinsa Ga Mutane Sama Da Dubu 125
https://parstoday.ir/ha/news/world-i379-kamfanin_twitter_ya_rufe_shafinsa_ga_mutane_sama_da_dubu_125
Sama Da Mutane dunbu 125 ne kamfanin sadarwar nan na Twitter ya rufewa shafinsa sanadiyar alakarsu da kungiyoyin 'yan ta'adda
(last modified 2018-08-22T06:57:46+00:00 )
Feb 06, 2016 08:20 UTC
  • Kamfanin Twitter Ya Rufe Shafinsa Ga Mutane Sama Da Dubu 125

Sama Da Mutane dunbu 125 ne kamfanin sadarwar nan na Twitter ya rufewa shafinsa sanadiyar alakarsu da kungiyoyin 'yan ta'adda

A wata sanarwa da ya fitar yau, Shafin yanar gizo na Twitter ya ce sama da Mutane dubu 125 ya rufewa shafinsa saboda yadda suke watsa Akidun ta'addanci a cikinsa, kuma mafi yawan su 'yan kungiyar ta'addancin nan na ISIS.

kamfanin ya ce cikin watanin takwas din nan na karshe, wadannan Mutane sun fadada aiyukan su, kuma wannan babbar barazana ne ga kamfanin.

A cewar wasu kafafen watsa labarai, kamfanin ta Twitter ya zamanto wani dandalin yada Akidun ta'addanci, inda a ko wata rana ake kaiwa duban Mutane sakonni domin kiransu ga shiga cikin kungiyar ISIS.