Shugaban Rasha Ya Tattauna Da Shugaban Siriya Kan Rikicin Kasar
A wata tattaunawa ta wayar tarho da suka yi a tsakaninsu, shugabannin kasashen Rasha da Siriya sun yi musayen ra'ayi a tsakaninsu kan yadda za a magance rikicn da ya ki ci ya ki cinyewa a kasar Siriyan.
Kamfanin dillancin labaran kasar Rasha Ita-Tas ya jiyo kakakin fadar Kremlin, fadar mulkin kasar Rashan Dmitry Peskov yana fadin cewa shugaba Vladimir Putin na kasar Rashan ya tattauna da takwararsa na kasar Siriya Basshar al-Asad dangane da yarjejeniyar tsagaita wuta a kasar Siriya da aka cimma tsakanin Rasha da Amurka inda suka bayyana hakan a matsayin wani mataki mai muhimmanci da zai iya kawo karshen zubar da jinin da ke faruwa a kasar.
Har ila yau shugabannin biyu sun jaddada aniyarsu ta aiki tare wajen ganin an tabbatar da tsagaita wutar
A shekaran jiya Litinin ne dai John Kerry Sakataren wajen kasar Amurka da takwararsa na kasar Rashan Sergei Lavrov suka sanar da yarjejeniyar da suka cimma ta tsagaita wuta a kasar Siriyan.