Amurka : Trump Da Sanders Sun Lashe Zaben Fidda Gwani
https://parstoday.ir/ha/news/world-i562-amurka_trump_da_sanders_sun_lashe_zaben_fidda_gwani
Hakan ya tabbatar da jagorancin Trump a takarar Jam’iyar Republican yayin da Bernie Sanders ya bada mamaki wajen kayar da Hillary Clinton.
(last modified 2018-08-22T06:57:47+00:00 )
Feb 10, 2016 08:26 UTC
  • Donal Trump da Benie Sanders
    Donal Trump da Benie Sanders

Hakan ya tabbatar da jagorancin Trump a takarar Jam’iyar Republican yayin da Bernie Sanders ya bada mamaki wajen kayar da Hillary Clinton.

A Amurka Donald Trump da Bernie Sanders sun lashe zaben fidda gwanin dan takaran shugabancin kasar da a ka gudanar a Jihar New Hampshire.

Nasarorin sun tabbatar da jagorancin Trump a takarar Jam’iyar Republican yayin da Bernie Sanders ya bada mamaki wajen kayar da Hillary Clinton wadda ake hasashen cewar za ta samu nasara kafin zaben.

Tsohuwar sakatariyar gwamnatin Amurka Cliton tayi na'am da kayan data sha a zaben na daren jiyya Talata, tareda shan alwashin ci gaba da aiki tukuru musamen a bangaren matasa.