• Nijeriya: An Sake Gano Wasu Dala Miliyan 151 Da Aka Sace A Kasar

    Nijeriya: An Sake Gano Wasu Dala Miliyan 151 Da Aka Sace A Kasar

    Feb 12, 2017 17:15

    Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da gano wasu makudan kudade da aka sace daga asusun gwamnatin da yawansu ya kai dala miliyan 150 da kuma wasu Naira biliyan takwas ta hanyar tsarin da gwamnatin kasar ta fito da shi na ba da tukwici ga wadanda suka tona asirin mutanen da suka wawure kudaden gwamnati.

  • JNI Da CAN Sun Yi Watsi Da Kiran Osinbajo Yayi Murabus, Sun Bukaci Addu'a Ga Buhari

    JNI Da CAN Sun Yi Watsi Da Kiran Osinbajo Yayi Murabus, Sun Bukaci Addu'a Ga Buhari

    Feb 10, 2017 05:40

    Manyan kungiyoyin musulmi da kirista a Nijeriya (wato Jama'atul Nasril Islam (JNI) da kuma Christian Association of Nigeria (CAN) sun yi kira ga illahirin magoya bayansu da su taya shugaban kasar Muhammad Buhari addu'ar samun sauki suna masu watsi da kiraye-kirayen da wasu suke yi ga mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo da yayi murabus.

  • Obasanjo Ya Soki Masu Yada Jita-Jitan Mutuwar Shugaba Buhari

    Obasanjo Ya Soki Masu Yada Jita-Jitan Mutuwar Shugaba Buhari

    Feb 04, 2017 05:36

    Tsohon shugaban Nijeriya Chief Olesegun Obasanjo yayi kakkausar suka ga masu yada jita-jitan cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari ya rasu yana mai bayyana hakan a matsayin cin amanar kasa.

  • Buhari Ya Tura Tawagar Jaje Ga Iyalan Da Harin Soji Ya Ritsa Da Su A Sansanin 'Yan Gudun Hijira

    Buhari Ya Tura Tawagar Jaje Ga Iyalan Da Harin Soji Ya Ritsa Da Su A Sansanin 'Yan Gudun Hijira

    Jan 18, 2017 17:32

    Fadar shugaban Nijeriya ya sanar da cewa shugaban Nijeriyan Muhammadu Buhari ya tura wata tawaga ta manyan jami'an gwamnatin kasar zuwa jihar Borno don isar da jaje da iyalai da 'yan'uwan mutanen da wani hari bisa kuskure da jiragen yakin sojin sama na Nijeriyan suka kai wa wasu 'yan gudun hijira da suke sansanin 'yan gudun hijiran da ke Rann kusa da kan iyakar kasar da Kamaru.

  • Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Ta Gano Ma'aikatan Boge Dubu 50 A Kasar

    Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Ta Gano Ma'aikatan Boge Dubu 50 A Kasar

    Dec 28, 2016 11:21

    Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da cewa ta gano ma’aikatan boge akalla dubu 50 a fadin kasar wanda hakan ya ba wa gwamnatin tarayyar damar tsimin kudaden da yawansu ya kai Naira biliyan 200 tsawon wannan shekara ta 2016 da ke karewa.

  • Sojojin Nijeriya Sun Kwace Tungar Boko Haram Na Karshe A Dajin Sambisa

    Sojojin Nijeriya Sun Kwace Tungar Boko Haram Na Karshe A Dajin Sambisa

    Dec 24, 2016 16:45

    Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya sanar da cewa sojojin kasar sun sami nasarar fatattakar 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram daga babbar maboyarsu a dajin Sambisa wadda ke a matsayin wata alama ta kawo karshen 'yan ta'addan.

  • Amsar Jammeh  Ga ECOWAS: Ba Zan Sauka Daga Karagar Mulki Ba

    Amsar Jammeh Ga ECOWAS: Ba Zan Sauka Daga Karagar Mulki Ba

    Dec 22, 2016 05:50

    Shugaban Gambiya Yahya Jammeh ya yi watsi da kokarin da shugabannin kungiyar tattalin arziki na Yammacin Afirka (ECOWAS) suke yi na sasanta rikicin siyasar kasar, yana mai cewa babu abin da zai sa shi sauka daga karagar mulkin kasar.

  • ECOWAS Ta Nada Buhari A Matsayin Babban Mai Shiga Tsakani A Rikicin Gambiya

    ECOWAS Ta Nada Buhari A Matsayin Babban Mai Shiga Tsakani A Rikicin Gambiya

    Dec 18, 2016 05:30

    Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) ta zabi shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a matsayin babban mai shiga tsakani don magance takaddamar siyasar da ta kunno kai a kasar Gambiya bayan kin amincewar da sakamakon zaben shugaban kasar da shugaba Yahya Jammeh yayi.

  • Buhari Ya Kirayi Al'ummar Nijeriya Da Su Kara Hakuri Da Gwamnatinsa

    Buhari Ya Kirayi Al'ummar Nijeriya Da Su Kara Hakuri Da Gwamnatinsa

    Dec 12, 2016 11:03

    Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya kirayi 'yan kasar da kada su yanke kauna dangane da karfin da gwamnatinsa take da shi na kyautata rayuwarsu, yana mai cewa kasafin kudin shekara ta 2017 da ya gabatar na dauke da matakan da za su iya fitar da kasar daga cikin matsalar karayar tattalin arziki da ake fuskanta.

  • An Sake Dage Shari'ar Da Ake Yi Wa Kanar Dasuki Zuwa 25 Ga Watan Janairun Badi

    An Sake Dage Shari'ar Da Ake Yi Wa Kanar Dasuki Zuwa 25 Ga Watan Janairun Badi

    Dec 07, 2016 17:08

    An sake dage shari'ar da ake yi wa tsohon mai ba wa shugaban kasar Nijeriya shawarar kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki (rtd) tare da wasu mukarrabansa bisa zargin sama da fadi kan kudaden sayen makamai da aka waye har zuwa ranar 25 ga watan Janairu na shekara mai kamawa saboda rashin lafiyar daya daga cikin wadanda ake zargin.