Amsar Jammeh Ga ECOWAS: Ba Zan Sauka Daga Karagar Mulki Ba
Shugaban Gambiya Yahya Jammeh ya yi watsi da kokarin da shugabannin kungiyar tattalin arziki na Yammacin Afirka (ECOWAS) suke yi na sasanta rikicin siyasar kasar, yana mai cewa babu abin da zai sa shi sauka daga karagar mulkin kasar.
Shugaba Jammeh ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi a lokacin da yake ganawa da tawagar kungiyoyin lauyoyi ta Afirka inda ya cewa shi ba matsoraci ba ne don haka babu wani da zai tauye masa hakkinsa ko razana shi. Shugaban ya ci gaba da cewa lalle shi ba zai yi cuta ba amma kuma ba zai bari wani ya cuce shi ba.
Shugaban ya zargi shugabannin kasashen kungiyar ta ECOWAS da suka ziyarci kasar a kwanakin baya don sasanta rikicin zaben da nuna goyon bayan bangare guda inda ya ce ya gabatar musu da dukkanin takardun da suke nuni da cewa an tafka magudi a zaben amma duk da haka suna matsa masa ya sauka inda ya ce da man tun kafin su zo kasar su riga da sun dauki matsayi cewar dole ya sauka daga mulki tun ma kafin su zo.
Kungiyar ta ECOWAS din dai wacce suka nada shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a matsayin babban mai shiga tsakanin kungiyar kan rikicin kasar Gambiyan, sun tsaya cewa wajibi ne shugaba Jammeh ya sauka daga karagar mulkin don bada damar rantsar da Adama Barrow a matsayin sabon shugaban kasar a ranar 19 ga watan Janairu mai kamawa.