-
Hukumar UNAIDS Ta Yaba Wa Gwamnatin Nijeriya Kan Kokarin Dakile Cutar AIDS
Dec 05, 2016 02:15Hukumar kula da cutar AIDS na Majalisar Dinkin Duniya (UNAIDS) ta yaba wa shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya dangane da kaddamar da wani sabon shirin da zai taimaka wajen kara kaimin fada da cutar kanjamau (AIDS) a kasar.
-
Buhari Ya Yaba Wa Sojojin Nijeriya Saboda Kwato Wata 'Yar Chibok
Nov 06, 2016 14:07Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya jinjinawa sojojin kasar saboda nasarar da suka samu wajen kwato daya daga cikin 'yan matan Chibok din nan da 'yan Boko Haram suka sace sama da shekaru biyun da suka gabata.
-
Buhari Ya Sake Jaddada Aniyar Gwamnatinsa Na Dawo Da Sauran 'Yan Matan Chibok Gida
Oct 19, 2016 13:35Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya sake jaddada aniyar gwamnatinta ta kwatowa da kuma dawo da sauran 'yan matan makarantar Chibok da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace su daga makarantarsu da ke garin Chibok din a jihar Borno sama da shekaru biyun da suka gabata.
-
Buhari Yayi Umurnin Sai Da Jirage 2 Na Fadar Shugaban Kasa Don "Rage Hasarar Da Ake Yi"
Oct 05, 2016 07:28Gwamnatin Nijeriya ta tallata jirage biyu daga cikin rukunan jiragen da suke fadar shugaban kasar a kokarin da gwamnatin ta ke yi na rage irin hasara da barnar kudin da ake yi wajen kula da jiragen.
-
Buhari: Sojojin Nijeriya Na Samun Gagarumar Ci Gaba A Fada Da Boko Haram
Sep 21, 2016 08:35Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar sojojin kasar suna ci gaba da samun gagarumar nasarar a fadar da suke yi da kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram.
-
Buhari Ya Ba Da Umurnin Kama Jami'an Da Ake Zargi Da Sace Abincin 'Yan Gudun Hijira
Sep 01, 2016 12:49Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ba wa 'yan sandan kasar umurnin kama jami'an gwamnatin da ake zargi da sace kayayyakin abincin da aka shirya kai wa ga 'yan gudun hijiran da rikicin Boko Haram ya tarwatsa a arewa maso gabashin kasar don ya zamanto darasi ga masu tunanin yin haka nan gaba.
-
An Kashe Wasu Sojojin Nijeriya Uku A Yankin Naija Delta
Aug 08, 2016 13:48Rahotanni daga Nijeriya na nuni da cewa wasu 'yan bindiga dadi sun kashe wasu sojoji uku a wani harin da suka kai musu a garin Nembe da ke jihar Bayelsa a yau din nan Litinin.
-
Wani Sabon Rikicin Na Kokarin Bullowa Tsakanin Gwamnati Da Majalisar Dattawan Nijeriya
Jun 20, 2016 06:35Wani sabon rikici na kokarin kunno kai tsakanin majalisar dattawan Nijeriya da gwamnatin kasar bayan da majalisar ta zargi gwamnatin da yin bita-da-kulli ga ayyukan majalisar da kuma kokarin sauya shugabancin majalisar.
-
Fadar Shugaban Nigeria Ta Bukaci Addu'a Ga Shugaba Buhari
Jun 06, 2016 13:14Fadar shugaban Nijeriya ta bukaci illahirin al'ummar kasar da su sanya shugaba Muhammadu Buhari cikin addu'a a daidai lokacin da ya ke fara wani hutu na kwanaki 10 don tafiya birnin London don neman maganin ciwon kunnen da ya ke fama da shi da ya hana shi gudanar da wasu ayyukan da aka tsara zai gudanar.
-
Buhari Ya Soke Ziyayar Niger Delta/ An Fara Share Dagolon Mai A Yankin Ogoni
Jun 02, 2016 12:48A yau Alhamis an kaddamar da shirin share dagolon man fetur da ya malala a yankin Ogoni na jihar Rivers a yankin Niger Delta mai arzikin mai karkashin jagorancin mataimakin shugaban Nijeriyan Yemi Osinbajo wanda ya wakilci shugaba Muhammadu Buhari a wajen bikin.