Hukumar UNAIDS Ta Yaba Wa Gwamnatin Nijeriya Kan Kokarin Dakile Cutar AIDS
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i14839-hukumar_unaids_ta_yaba_wa_gwamnatin_nijeriya_kan_kokarin_dakile_cutar_aids
Hukumar kula da cutar AIDS na Majalisar Dinkin Duniya (UNAIDS) ta yaba wa shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya dangane da kaddamar da wani sabon shirin da zai taimaka wajen kara kaimin fada da cutar kanjamau (AIDS) a kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:21+00:00 )
Dec 05, 2016 02:15 UTC
  • Hukumar UNAIDS Ta Yaba Wa Gwamnatin Nijeriya Kan Kokarin Dakile Cutar AIDS

Hukumar kula da cutar AIDS na Majalisar Dinkin Duniya (UNAIDS) ta yaba wa shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya dangane da kaddamar da wani sabon shirin da zai taimaka wajen kara kaimin fada da cutar kanjamau (AIDS) a kasar.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanar da ta fitar mai dauke da sanya hannun shugaban bangaren watsa labarai na hukumar a Nijeriya Mr Charles-Martin Jjuuko, inda ya ce sabbin shirye-shiryen da gwamnatin Tarayyar Nijeriyan ta shigo da su za su taimaka sosai wajen dakile yaduwar cutar ta AIDS a kasar.

A jiya Lahadi ne dai gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta kaddamar da wani shiri na mayar da martani na gaggawa ga cutar ta AIDS da kuma kara kyautata irin kular da ake ba wa masu cutar ta AIDS bugu da kari kan kokarin dakatar da yaduwar cutar.

Shi dai wannan shirin wanda ministan lafiya na Nijeriyan Prof. Isaac Adewole ya kaddamar a Abuja babban birnin Tarayyar kasar a madadin shugaba Buharin an yi shi ne don girmama ranar fada ta cutar ta AIDS ta duniya ta shekara ta 2016.