An Kashe Wasu Sojojin Nijeriya Uku A Yankin Naija Delta
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9355-an_kashe_wasu_sojojin_nijeriya_uku_a_yankin_naija_delta
Rahotanni daga Nijeriya na nuni da cewa wasu 'yan bindiga dadi sun kashe wasu sojoji uku a wani harin da suka kai musu a garin Nembe da ke jihar Bayelsa a yau din nan Litinin.
(last modified 2018-08-22T06:58:44+00:00 )
Aug 08, 2016 13:48 UTC
  • An Kashe Wasu Sojojin Nijeriya Uku A Yankin Naija Delta

Rahotanni daga Nijeriya na nuni da cewa wasu 'yan bindiga dadi sun kashe wasu sojoji uku a wani harin da suka kai musu a garin Nembe da ke jihar Bayelsa a yau din nan Litinin.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar 'yan bindigar wadanda suke sanye da riguna irin na limaman coci sun bude wuta wa sojojin ne inda bayan sun kashe su suka kwashe makamansu suka kuma tsere da wasu jiragen ruwan mallakin sojojin.

Majiyoyin sojin Nijeriyan dai sun ce tuni aka baza dakaru don neman wadannan mutanen.

Tun dai daga watan Fabrairun da ya gabata ne 'yan sabuwar kungiyar 'yan tsageran Naija Deltan da ake kira da Avengers suka matsa kaimi wajen kai hare-hare yanki da  fasa bututan man fetur lamarin da ke ci gaba da yin kafar ungulu ga tattalin arzikin kasar da ya dogara kusan kacokam kan man fetur din da ake sayarwa.

Gwamnatin tarayyar Nijeriyan dai ta sha sha alwashin murkushe wadannan masu tayar da kayar bayar.