-
Shugaba Buhari Zai Kai Ziyara Yankin Niger-Delta
May 31, 2016 00:51Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyara yankin Niger Delta mai arzikin man fetur a ranar Alhamis mai zuwa don kaddamar da shirin nan da aka jima ana dakonsa na tsarkake yankin da ke fuskantar tsananin gurbatar yanayi sakamakon kwararar man fetur da ake fuskanta a yankin.
-
Shugaba Buhari Ya Bukaci 'Yan Nijeriya Da Su Kara Hakuri Da Gwamnatinsa
May 29, 2016 10:37Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yabi 'yan kasar saboda irin hakuri da juriyar da suka nuna tsawon shekara guda na mulkinsa duk kuwa da matsalolin da ake fuskanta yana mai kiransu da su kara hakuri da shirin gwamnatin nasa da gyara kasar.
-
Buhari Ya Ba Da Umurnin Kara Tura Sojoji Yankin Niger Delta Don Fada Da Tsagera
May 21, 2016 00:40Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya ce ya ba da umurnin kara tura sojoji yankin Niger-Delta don fada da 'yan tsageran yankin da suke ci gaba da kai hare-hare kan bututun mai da iskar gas lamarin da ke ci gaba da zagon kasa ga tattalin arzikin kasar da ke cikin mawuyacin hali.
-
Buhari Ya Sha Alwashin Daukar Tsauraran Matakai Kan Masu Fasa Bututun Mai Na Niger-Delta
Apr 14, 2016 00:13Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya sha alwashin daukan tsauraran matakan ba sani ba sabo kan mutanen da suke hannu cikin hare-haren baya-bayan nan kan batutun man fetur da iskar gas na a yankin Niger-Delta mai arzikin man fetur.
-
Buhari Ya Taya Mutanen Da Gobarar Kasuwanni Kano Da Kebbi Ta Ritsa Da Su Jaje
Mar 27, 2016 10:55Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya bayyana alhini da kuma juyayinsa dangane da gobarar da ta faru a kasuwar sabon gari da ke jihar Kano da kuma ta babbar kasuwar birnin Kebbi ta jihar Kebbi inda ya kirayi gwamnatocin jihohin biyu da su dau matakan da suka dace wajen hana sake faruwar hakan.
-
Kotu Ta Ba Da Belin Alex Badeh Tsohon Hafsan Hafsoshin Sojojin Nijeriya
Mar 10, 2016 14:38Wata babbar kotun tarayya a Abuja, babban birnin Tarayyar Nijeriya, ta bayar da belin tsohon hafsan hafsoshin sojin kasar , Air chief Marshal Alex Badeh bisa wasu tsauraran sharuddan da wajibi ne ya cika su kafin a sake shi daga gidan yarin da ake tsare da shi.
-
Shugaba Zuma Zai Fara Ziyarar Aiki A Nijeriya A Yau Talata
Mar 08, 2016 02:15A yau Talata ne ake sa ran Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma zai fara wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Nijeriya a bisa gayyatar da takwararsa na Nijeriyan Muhammadu Buhari yayi masa don karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
-
Buhari Ya Sallami Shugabannin Hukumomi 26 Na Tarayyar Kasar
Feb 16, 2016 02:19Fadar shugaban Nijeriya ta sanar da korar shugabanin wasu hukumomi da ma'aikatun gwamnatin tarayyar kasar su 26, bugu da kari kan nada wasu sabbi da za su ci gaba da rike ma'aikatu da hukumomin na wucin gadi har lokacin da za a tabbatar da su ko kuma nada wasu sabbi.
-
Afirka: Ziyarar Shugaba Buhari Na Najeriya A Tehran
Feb 04, 2016 04:14Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri an Afirka a mako.