Shugaba Buhari Zai Kai Ziyara Yankin Niger-Delta
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6019-shugaba_buhari_zai_kai_ziyara_yankin_niger_delta
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyara yankin Niger Delta mai arzikin man fetur a ranar Alhamis mai zuwa don kaddamar da shirin nan da aka jima ana dakonsa na tsarkake yankin da ke fuskantar tsananin gurbatar yanayi sakamakon kwararar man fetur da ake fuskanta a yankin.
(last modified 2018-08-22T06:58:22+00:00 )
May 31, 2016 00:51 UTC
  • Shugaba Buhari Zai Kai Ziyara Yankin Niger-Delta

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyara yankin Niger Delta mai arzikin man fetur a ranar Alhamis mai zuwa don kaddamar da shirin nan da aka jima ana dakonsa na tsarkake yankin da ke fuskantar tsananin gurbatar yanayi sakamakon kwararar man fetur da ake fuskanta a yankin.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar a wata sanarwa da mahukuntan Nijeriyan suka fitar a jiya Litinin an bayyana cewar a ranar Alhamis mai zuwa ne shugaba Buharin zai kai ziyarar don kaddamar da shirin tsarkake yankin daga matsalar gurbatar yanayi da yake fuskanta don magance wa mutanen yankin daya daga cikin manyan matsalolin da ke damunsu.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai, shugaba Buharin ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta tattauna da shugabannin yankin Niger Deltan don samo hanyar da za a magance musu matsaloli da korafe-korafen da suke da su.

Ziyarar ta shugaba Buhari ta zo ne a daidai lokacin lokacin da sabuwar kungiyar tsagerun yankin Niger Delta mai suna Niger Delta Avengers (NDA) suke ci gaba da kai hare-hare kan bututun man fetur da kuma kayayyakin kamfanonin da suke hako mai din a yankin lamarin da ke ci gaba da zagon kasa ga tattalin arzikin kasar.