Shugaba Zuma Zai Fara Ziyarar Aiki A Nijeriya A Yau Talata
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2128-shugaba_zuma_zai_fara_ziyarar_aiki_a_nijeriya_a_yau_talata
A yau Talata ne ake sa ran Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma zai fara wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Nijeriya a bisa gayyatar da takwararsa na Nijeriyan Muhammadu Buhari yayi masa don karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
(last modified 2018-08-22T11:27:57+00:00 )
Mar 08, 2016 05:45 UTC
  • Shugaba Zuma Zai Fara Ziyarar Aiki A Nijeriya A Yau Talata

A yau Talata ne ake sa ran Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma zai fara wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Nijeriya a bisa gayyatar da takwararsa na Nijeriyan Muhammadu Buhari yayi masa don karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

A wata sanarwa da fadar shugaban kasar Afirka ta Kudun ta fitar, ta ce babbar manufar ziyarar dai ita ce karfafa alaka tsakanin kasashen biyu ta bangarori daban-daban da suka hada da kasuwanci, aikin noma, tsaro da sauransu.

Har ila yau sanarwar ta ce a yayin ziyarar, shugaba Zuma zai gabatar da jawabi a majalisar Nijeriyan da zai hada dukkanin 'yan majalisun kasar biyu, wato majalisar dattawa da ta wakilai, kamar yadda kuma shi da takwararsa na Nijeriyan Muhammadu Buhari za su gabatar da jawabi a wajen wani taron hadin gwiwa na Nijeriya da Afirka ta Kudu kan kasuwanci.

Daga cikin wadanda ake sa ran za su rufa wa shugaba Zuman baya har da ministocin harkokin cikin gida, harkokin kasa da kasa, tsaro, albarkatun kasa, kasuwanci da kuma masana'antu, baya ga wasu 'yan kasuwa a lokacin da ake yi na kara farfado da alakar da ke tsakanin kasashen biyu wacce ta dan yi tsami a baya.