Kotu Ta Ba Da Belin Alex Badeh Tsohon Hafsan Hafsoshin Sojojin Nijeriya
Wata babbar kotun tarayya a Abuja, babban birnin Tarayyar Nijeriya, ta bayar da belin tsohon hafsan hafsoshin sojin kasar , Air chief Marshal Alex Badeh bisa wasu tsauraran sharuddan da wajibi ne ya cika su kafin a sake shi daga gidan yarin da ake tsare da shi.
Rahotanni daga Nijeriya sun ce Alkalin kotun mai shari'a Okon Ebang ya sanar da amincewar kotun na ta ba da belin Mr. Badeh bisa sharuddan da suka hada da biyan kudi Naira biliyan biyu da kuma kawo mutane biyu da za su tsaya masa wadanda kowanne zai bayar da Naira biliyan guda jingina, sannan kuma dole ne wadannan mutanen su kasance sun mallaki wata kadara a birnin Abujan, bugu da kari kuma ya mika passport dinsa na tafiya waje ga kotun.
Hukumar EFCC, mai fada da ta'annuti wa tattalin arzikin kasar ne dai ta gurfanar da Mista Badeh gaban wannan kotun a ranar Litinin din da ta gabata bisa zargin tafka laifuka 10 masu alaka da zamba cikin aminci da almundahanar biliyoyin nairori da aka ware don sayo makaman fada da kungiyar Boko Haram a lokacin tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan ta Nijeriyar; zargin da tsohon hafsan hafsoshin ya musanta.
Ba da belin dai ya biyo bayan bukatar hakan ne da lauyar wanda ake tuhuma din Samuel Zibiri ya shigar inda ya ce inda ake tsare da Mr. Badeh din a gidan yarin bai dace ba.