Buhari Ya Sallami Shugabannin Hukumomi 26 Na Tarayyar Kasar
Fadar shugaban Nijeriya ta sanar da korar shugabanin wasu hukumomi da ma'aikatun gwamnatin tarayyar kasar su 26, bugu da kari kan nada wasu sabbi da za su ci gaba da rike ma'aikatu da hukumomin na wucin gadi har lokacin da za a tabbatar da su ko kuma nada wasu sabbi.
A wata sanarwa da ministan watsa labarain kasar, Alhaji Lai Mohammed, ya fitar ya ce an kori shugabannin gidan talabijin na gwamnatin tarayya, (NTA) Mista Sola Omole, da na hukumar radiyon tarayya (FRCN) Malam Ladan Salihu, da muryar Nijeriya (VON) Mista Sam Worlu, da kamfanin dillacin labarai na kasa (NAN) Mista Ima Niboro, da da kuma Hukumar wayar da kan jama’a ta kasar (NOA) Mista Mike Omeri.
Har ila yau fadar shugaban ta Nijeriya kuma ta sanar da korar wasu shugabannin ma'aikatun gwamnatin su 20, inda fadar shugaban kasar ta ce shugaba Buharin ya gode musu saboda ayyukan da suka yi a baya.
An jima dai ana tsammanin shugaba Buharin zai yi wadannan sauye-sauyen don cimma manufarsa ta kawo sauyi a kasar. Wasu daga cikin jami'an da suka sallamar dai sun nuna godiyarsu ga shugaban kan yadda ya bar su a kan wadannan mukaman na su har tsawon watanni takwas da darewarsa karagar mulki duk kuwa da matsin lambar da suka ce yana fuskanta daga wasu 'yan jam'iyyarsa ta APC na ya cire su.