Wani Sabon Rikicin Na Kokarin Bullowa Tsakanin Gwamnati Da Majalisar Dattawan Nijeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6985-wani_sabon_rikicin_na_kokarin_bullowa_tsakanin_gwamnati_da_majalisar_dattawan_nijeriya
Wani sabon rikici na kokarin kunno kai tsakanin majalisar dattawan Nijeriya da gwamnatin kasar bayan da majalisar ta zargi gwamnatin da yin bita-da-kulli ga ayyukan majalisar da kuma kokarin sauya shugabancin majalisar.
(last modified 2018-08-22T06:58:28+00:00 )
Jun 20, 2016 06:35 UTC
  • Wani Sabon Rikicin Na Kokarin Bullowa Tsakanin Gwamnati Da Majalisar Dattawan Nijeriya

Wani sabon rikici na kokarin kunno kai tsakanin majalisar dattawan Nijeriya da gwamnatin kasar bayan da majalisar ta zargi gwamnatin da yin bita-da-kulli ga ayyukan majalisar da kuma kokarin sauya shugabancin majalisar.

Korafin 'yan majalisar dai yana cikin wata sanarwa ce da majalisar ta fitar dauke da sanya hannun kakakinta, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, inda ta yi zargin cewa gwamnati na shirin gurfanar da shugabannin majalisar, wato Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekeweremadu a gaban kotu bisa zargin yin zagon kasa tare da yin jabun dokokin majalisar.

Majalisar ta ce wannan matakin na bangaren zartarwar wani shiri ne na murkushe majalisar wanda hakan zai jefa dimokradiyyar kasar cikin hatsari.

A ranar 10 ga watan Yunin nan ne dai aka shigar da karar inda ake bukatar a gudanar da bincike dangane da zargin da ake yi zagon kasa tare da yin jabun dokokin majalisar a lokacin da aka gudanar da zaben shugabannin majalisar a shekarar da ta gabata.