Obasanjo Ya Soki Masu Yada Jita-Jitan Mutuwar Shugaba Buhari
Tsohon shugaban Nijeriya Chief Olesegun Obasanjo yayi kakkausar suka ga masu yada jita-jitan cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari ya rasu yana mai bayyana hakan a matsayin cin amanar kasa.
Chief Olusegun Obasanjo ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya bayyana masu yada wannan jita-jitar da cewa mutane ne da ba su san inda duniya ta dosa ba, yana mai cewa babu wani mutum mai cikakken hankali da zai aikata wannan aiki na yada jita-jitar mutuwa ga shugaba Buhari.
Tsohon shugaban Nijeriyan ya kirayi masu yada jita-jitar da cewa idan ma ba sa son shugaban Buharin ne to su bari sai lokacin zabe a shekara ta 2019 su fito su kada wa waninsa kuri'a.
Tun dai bayan da shugaba Buharin ya fara hutu a karshen watan Janairun da ya gabata wasu suke ta yada labarin cewa Allah yayi masa rasuwa, lamarin da fadar shugaban Nijeriyan ta musanta tana mai cewa shugaban yana nan da ransa, kuma a na sa ran a ranar 6 ga watan nan ma zai dawo bakin aikinsa.