Pars Today
A kasar Burundi kuma, wani jami'in dan sanda ne a cikin maye ya bude wuta kan jama'a inda ya kashe abokin aikinsa da kuma wasu fararen hula uku.
Gwamnatin kasar Burundi Ta Dakatar da ayyukan dukkan kungiyoyin bada agaji na kasashen waje wadanda suke aiki a cikin kasar.
Mahukuntan Burundi, sun sanar da dakatar da ayyukan kungiyoyin kasashen waje a cikin kasar, har zuwa lokacin da suka fara aiki da sabuwar dokar data tanadi sanya ido ga ayyukansu.
Gwamnatin kasar Burundi ta yi barazanar cewa matukar dai majalisar kare hakkokin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta ci gaba da shigo da siyasa cikin mu'amalar da take yi da ita, to kuwa za ta fice daga majalisar.
Gwamnatin kasar Burundi ta yi kakkausar suka kan masu bincike na kwamitin gudanar da bincike na MDD kan abinda ya shafi kare hakin bil-adama da suka bayar da rahoton kan kasar.
Kwamitin binciken Majalisar Dinkin Duniya kan kasar Burundi ya yi gargadi kan yadda cin zarafin bil-Adama ke yi kamari a kasar.
Gwamnatin Burundi ta sanar da kame jami'in gwamnatin a tare da wasu faransawa hudu bisa tuhumar almundahana ta kudade.
Shugaban kasar Burundi ya ce ba zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar a shekarar 2020 ba
Kotun tsarin mulki a kasar Burundi ta tabbatar da sakamakon zaben raba gardama da aka kada kuri'arsa a ranar 17 ga watan Mayu da ya gabata, kan yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima.
A Burundi, sakamakon zaben raba gardama da aka kada kuri'arsa ya nuna cewa mafi yawan 'yan kasar sun amince da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima.