Shugaban Burundi Ba Zai Sake Tsayawa Takara Ba.
Shugaban kasar Burundi ya ce ba zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar a shekarar 2020 ba
Tashar Talabijin din France 24 ta nakalto Pierre Nkurunziza Shugaban kasar Burundi na cewa duk da cewa ya nada hakkin sakewa tsayawa takara a sabon kundin tsarin milkin kasar da aka yiwa kwaskwarima, to amma ba zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar ba.
Shugaba Pierre Nkurunziza dake jawabi gaban magoya bayan sa da kuma jami’an diflomasiya, ya baiwa marada kunya wajen sanar musu da cewar ba zai yi amai ya lashe ba, wajen sake takarar shugaban kasar, inda yake cewa wa’adin mulkin sa zai kare a shekarar 2020, kuma daga wannan babu sabuwar takara.
Sai dai yan adawa sun bayyana rashi gamsuwar su tareda nuna shaku dangane da wadanan kalamai daga Shugaban kasar Pierre Nkurunziza.
A ranar 17 ga watan Mayun da ya gabata ne aka gudanar da zaben raba gardama na yiwa kundin tsarin milkin kasar kwaskwarima, inda ya samu amincewa da kashi63%, wanda 'yan adawa ke ganin cewa an yi hakan ne domin a bawa shugaba Nkurunziza damar ci gaba da dawwama kan karagar mulki har zuwa shekara ta 2034.