Pars Today
Rahotanni daga kasar Chadi na cewa an gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na farko a cikin kwanciyar hankali da lumana.
A yau Lahadi ne al'ummar Chadi suke gudanar da zaben shugaban kasa tsakanin shugaba mai ci Idris Deby da wasu 'yan takara goma sha biyu daga jam'iyyun adawar kasar.
Shugaban Hamayyar Siyasa A Kasar Chadi Ya yi Gargadi Akan Rikicin Siyasa
Yan adawa a kasar Chadi sun nuna adawarsu da shirin shugaban kasar na kokarin yin tazarce a kan karagar shugabancin kasar ta hanyar gudanar da yajin aiki da rashin fitowa harkokin yau da kullum a jiya Laraba.
Rahotanni daga kasar Chadi sun bayyana wasu yara 'yan makaranta a kasar sun rasa rayukansu wasu kuma sun sami raunuka sakamako harin da 'yan sanda suka kai musu a lokacin da suke zanga-zanga.
Kungiyoyin fararen hula da na kwadago a kasar Chadi sun fito fili sun bayyana adawarsu da shirin tazarcen shugaban kasar a kan karagar mulki bayan shafe tsawon shekaru fiye da 25 yana shugabancin kasar.
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa ta aike da kayayyakin abinci ga dubban 'yan gudun hijirar kasar Chadi da rikicin kungiyar Boko Haram ya tarwatsa su.
Shugaba Idriss Deby na kasar Chadi ya nada Pahimi Padacke Albert a matsayin sabon Firaministan kasar biyo bayan murabus din da tsohon firayi ministan kasar Kalezeube Pahimi Deubet yayi.
Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya yi alkawarin cewa; Idan har al'ummar kasar suka sake zabensa a matsayin shugaban kasa zai dauki matakin kyaiyade wa'adin shugabancin kasar.
A ranar 10 ga watan Afrilu mai zuwa al'umma a kasar Chadi ke kada kuri'a a zaben shugaban kasa.