Gargadi Akan Rikicin Siyasa A Kasar Chadi
(last modified Thu, 03 Mar 2016 07:48:05 GMT )
Mar 03, 2016 07:48 UTC
  • Gargadi Akan Rikicin Siyasa A Kasar Chadi

Shugaban Hamayyar Siyasa A Kasar Chadi Ya yi Gargadi Akan Rikicin Siyasa

Kamfanin Dillancin Labarun (AFP) ya ambato shugaban hamayyar siyasa na Kasar Chadi, Saleh Kebzabo da ya ke ziyara a kasar Faransa yana cewa; Adaidai lokacin da ake karatar zaben shugaban kasar a cikin watan Aprilu, da akwai yiyuwar tashin rikicin siyasa a kasar ta Chadi.

Saleh Kebzabo ya ci gaba da cewa; Al'ummar kasar ta Chadi, ba za su amince da magudin zabe ba, sannan ya kara da cewa; Me zai sa a ce kasa kamar Chadi wacce ta ke da arzikin man fetur, ta fada cikin rikicin siyasa.

Shugaban hamayyar ya zargi shugaba mai ci a yanzu Idris Deby da cewa ya yi magudi a zaben da ya gabata.

A makon da ya shude 'yan hamayyar siyasar kasar ta Chadi sun gudanar da Zanga-zangar kin amincewa da kokarin shugaban Idris Deby na yin tazarce, abinda ya haddasa tsaikon ayyukan a cikin birnin Ndjamena da kuma wasu gagaruruwan kasar.