Shugaban Kasar Chadi Idris Deby Ya Nada Sabon Firayi Ministan Kasar
Shugaba Idriss Deby na kasar Chadi ya nada Pahimi Padacke Albert a matsayin sabon Firaministan kasar biyo bayan murabus din da tsohon firayi ministan kasar Kalezeube Pahimi Deubet yayi.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa a wata sanarwa da fadar shugaban kasar Chadin ta fitar ta bayyana cewar shugaba Deby na nada Pahimi Padacke Albert a matsayin sabon firayi ministan kasar kuma shugaban gwamnati.
Duk da cewa sanarwar ba ta yi karin bayani dangane da dalilan murabus din tsohon firayi ministan ba, amma dai wasu majiyoyi suna nuni da cewa murabus din ya biyo sabanin da ya kunno kai ne tsakanin shugaba Deby da tsohon firayi minista bisa kokarin shugaba Deby na sake tsayawa takara a zaben shugabancin kasar da za a gudanar a ranar 10 ga watan Afrilu mai zuwa.
Shugaban Idris Deby ya dare karagar mulkin kasar Chadin ne a wani juyin mulki da yayi wa tsohon shugaban kasar Hissen Habre a shekarar 1990, kuma tun a lokacin yake mulkin kasar. Idan har ya lashe zaben da za a yi din zai zamanto yana cikin wa’adi na biyar na shugabancin kasar.