Pars Today
Rasha ta ce za ta meka jiragen yaki samfarin Sukhoi Su-35 guda 10 a cikin wannan shekara ta 2018
Babban bankin Nijeriya (CBN) ya kulla wata yarjejeniya ta musayar kudi da babban bankin kasar China na kudaden da suka kai Dala biliyan 2.36 da nufin karfafa harkar kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.
Karamin jakadan China a kasar Libiya ya bayyana goyon bayan kasarsa na shirin MDD wajen warware rikicin kasar Libiya ta hanyar tattaunawa.
Shugaban kasar Zimbabwe ya jinjinawa kasar China kan irin goyon bayan da take bai wa Zimbabwe musamman a fuskar tattalin arziki da siyasa tare da bayyana aniyar kasarsa ta ci gaba da karfafa alaka da kasar ta China a bangarori da dama.
Shugaban kasar China Xi Jinping zai ci gaba da mulkin kasar har illa Masha Allahu, bayan da jam'iyya mai mulki ta amince da hakan.
Shugaban kungiyar Tarayyar Afrika ya jaddada cewa: Zargin cewar kasar China tana gudanar da ayyukan leken asiri kan kungiyar tarayyar Afrika kokari ne na rusa kyakkyawar alakar da ke tsakanin bangarorin biyu.
Kwamitin Kungiyar Tarayyar Afirka ta karyata labarin da ake watsawa na cewa kasar China tayi yiwa kungiyar leken asiri ta hanyar kutse a Na'urorin hedkwatar kungiyar.
Kasar Faransa ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu Cibiyoyi da jami'ai su 25 kan zargin taimakawa shirin Siriya na sarafawa da kuma kera makamai masu guba.
A yau Litinin, shugaban Faransa Emmanuel Macron ke fara ziyarar kwanaki uku a China, in da ake sa ran zai kulla wata alaka ta musamman da gwamnatin kasar don yaki da ta’addanci da kuma magance matsalar dumamar yanayi a duniya.
Bayan watsa labarin cinikayyar Man fetir tsakanin buranan Beijing da Pyongyang, Shugaban Amurka Donal Trump ya zargi hukumomin China da karya takunkumin da MDD ta kakabawa Korea ta Arewa ta hanyar sayar mata da man fetir.