China Ta Bayyana Goyon Bayanta Na Shirin MDD Wajen Warware Rikicin Libiya.
Karamin jakadan China a kasar Libiya ya bayyana goyon bayan kasarsa na shirin MDD wajen warware rikicin kasar Libiya ta hanyar tattaunawa.
Kamfanin dillancin labaran Xin huwa na kasar Sin ya nakalto Wang Cayman karamin jakadan kasar Sin a Libiya a yayin ganawarsa da Khalid al mashri sabon shugaban kwamitin koli na gwamnatin kasar na cewa shirin da Majalisar dinkin duniya ta gabatar na warware rikicin kasar ta hanyar siyasa da kuma gudanar da zaben shugaban kasa gami da na 'yan majalisar dokoki a kan lokaci ita ce hanya da ya kamata a bi, kuma kasar na goyon bayan wannan shiri.
A cikin wani shiri da ya gabatar, manzon musaman na MDD a kasar Libiya ya bukaci gudanar da zaben shugaban kasa gami da na 'yan majalisa kafin karshen wannan shekara ta 2018.
Har ila yau karamin jakadan na China a Libiya, ya bayyana goyon bayansa na gudanar da taron kasa a wasu gariruwan kasar da nufin tattaunawa da kuma lalubo hanyar magance rikici da kasar ke fama da shi.
A shekarar 2011 ne kasar Libiya ta fada cikin rikici bayan da Dakarun tsaron Nato suka kifar da gwamnatin kanal Mu'ammar Kaddafi.