Shugaban Kasar Faransa Ya Fara Ziyara A China
(last modified Mon, 08 Jan 2018 19:13:54 GMT )
Jan 08, 2018 19:13 UTC
  • Shugaban Kasar Faransa Ya Fara Ziyara A China

A yau Litinin, shugaban Faransa Emmanuel Macron ke fara ziyarar kwanaki uku a China, in da ake sa ran zai kulla wata alaka ta musamman da gwamnatin kasar don yaki da ta’addanci da kuma magance matsalar dumamar yanayi a duniya.

A Wannan Litinin ne Shugaba Emmanuel Macron na Faransa  ya  fara ziyarar aiki a birnin Xian na China inda ya fara ziyarar wannan birni mai tarihi gabannin gabatar da jawabinsa da zai tabo dangantaka tsakanin China da Faransa.

Shugaba Macron da ya fara ziyarar ta kwanaki uku a wannan birni bisa jagorancin mai masaukin bakinsa Shugaba Xi Jinping na China inda za su mayar da hankali kan batutuwa da suka shafi tsare-tsare na kasuwanci tsakanin kasashe na yankin Asiya da takwarorinsu na kasashen Turai ta hanyar musayar kayayyaki na kasuwanci da bin  hanyoyin ruwa da jiragen kasa da na mota.

Hari ila yau ana sa ran Shugaba  Macron zai nemi hadin kai daga China don ganin cewa ta taka rawa ta musamman wajen aiwatar da yarjejeniyar birnin Paris da aka cimma don yaki da sauyin yanayi bayan gwamnatin Amurka karkashin Shugaba Donald Trump ta tsame kanta daga yarjejeniyar.