Pars Today
Kasashen Rasha da China sun kalubalanci tsarin tsaron Amurka da shugaba Trump ya gabatar a Jiya Litini, wanda ya ce kasashen biyu na a matsayin babban abun damuwarsa.
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce yana da yakini akan samun mafita kan rikicin Koriya ta Arewa.
Shugaban kasar China Xi Jinping ya bukaci rundunar sojojin ruwan kasar ta farko a kasashen waje da ta yi aiki tukuru don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin kahon Afrika da suka yi sansani da kuma duniya gaba daya.
Jakadan Kasar Sin a Angola ya ce; Sabbin ayyukan raya kasa da Sin ta yi a kasar a cikin 2017 sun haura dalar Amurka biliyan 10.
Kwamandan sojan China a kasar Djibouti Liang Yang ya ce; Sojoji masu yawa ne suke atisayen domin samun karin kwarewar aiki da kuma sarrafa sabbin na'urori.
Rahotanni daga China na cewa akalla mutane 13 ne suka rasa rayukansu a wata girgiza kasa mai karfin maki 6,5 data aukawa kasar a jiya Talata.
Ministan harkokin wajen kasar China Wang Yi ya bayyana cewar kasar Chinan ta yi alkawarin taimakawa kasar Gambiya a bangaren ayyukan gona, yawon shakatawa da sauran fannoni.
Kasar china ta kafa sansanin sojin ruwa na farko a kasashe wajen a kasar Djibouti.
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce ba zai lamunta ko kadan ba da yadda kasar China bata daukar wani ba mataki ba kan Koriya ta Arewa.
Wakilin China a MDD ya nuna adawa dangane da daukar matakin Soja kan kasar Koriya ta Arewa.