Rasha Da China Sun Kalubalanci Tsarin Tsaron Amurka
Kasashen Rasha da China sun kalubalanci tsarin tsaron Amurka da shugaba Trump ya gabatar a Jiya Litini, wanda ya ce kasashen biyu na a matsayin babban abun damuwarsa.
Wata sanarwa da gwamnmatin Rasha ta fitar ta bakin kakakinta, Dmitri Peskov, ta ce kasar ba zata lamunta da irin wadanan kalaman ba na cewa babbar barazana ce ga tsaron Amurka.
Ita ma a nata bangare kasar China ko Sin ta fitar da makamanciyar wannan sanarwa a yau, tana mai kalubalantar tsarin tsaron na Amurka da Trump ya gabatar a matsayin yakin ''cacar baki'', tana mai cewa kuma ba zata iya jurewa duk wani yunkuri na canza fasalin dabaru da manufofinta ba.
A jiya ne dai da yake bayyana sabuwar dabararsa ta tsaron kasa a cikin wani jawabi da ya gabatar a birnin Washington, Trump ya bayyana Rasha da China a matsayin babban damuwarsa, yana cewar kasashen biyu suna kalubalantar darajar Amurka da tasirinta da kuma arzikinta.