Girgiza Kasa Ta Kashe Mutane Da Dama A China
https://parstoday.ir/ha/news/world-i23026-girgiza_kasa_ta_kashe_mutane_da_dama_a_china
Rahotanni daga China na cewa akalla mutane 13 ne suka rasa rayukansu a wata girgiza kasa mai karfin maki 6,5 data aukawa kasar a jiya Talata.
(last modified 2018-08-22T11:30:31+00:00 )
Aug 09, 2017 06:30 UTC
  • Girgiza Kasa Ta Kashe Mutane Da Dama A China

Rahotanni daga China na cewa akalla mutane 13 ne suka rasa rayukansu a wata girgiza kasa mai karfin maki 6,5 data aukawa kasar a jiya Talata.

Bayanai daga kasar dai sun ce an samu girgizar kasa har sau biyu cikin kasa da sa'o'i 24.

Ko baya ga wadanda suka mutu da akwai wasu sama da 60 da suka jikkata a larduna Xinjian da Sichuan.

Saidai wasu rahotanni na daban sun ce mai yi wa adadin wadanda suka mutun ya karu.

Lardin Sichuan yanki ne dai dake fuskantar barazanar yawan afkuwar girgizar kasa.

Ko a shekara 2008 mutane fiye da 70,000 suka mutu a wata girgizar kasar a yankin.