China Ta Kafa Sansanin Sojan Ruwa A Kasar Djibouti
Kasar china ta kafa sansanin sojin ruwa na farko a kasashe wajen a kasar Djibouti.
Kamfanin dillancin labaran Arab News na kasar Saudiya ya habarta cewa a kokarinta na bunkasa harakokin tsaronta a duniya, kasar China ta kafa sansanin sojin ruwa na farko a kasashen waje a Djibouti, wannan kuma na zuwa ne a yayin da kasar ke bikin cika shekaru 90 da kafa rundunar tsaron kasar.
Aiki tare tsakanin kasa da kasa, gudanar da atisayin soja, bayar da horo na musaman ga masu aikin ceton gaggauwa ga jiragen da suka fada cikin hatsarin tsaro, na daga cikin dalilin da kasar China ta bayar na kafa wannan sansanin sojan ruwa a kasar ta Djibouti.
A yayin da take mayar da martani a kan sukar kafa wannan sansani, Gwamnatin ta China ta tabbatar da cewa kafa wannan sansani zai bayar da guduma sosai wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a ruwan kasa da kasa, ko bayan ga kasar ta China, kasashen Amurka , Japon da Faransa su nada sansanin Soja a ruwan kasar na Djibouti.