Sojojin Kasar Sin, Suna Gudanar Da Atisaye A Kasar Djibouti:
(last modified Tue, 26 Sep 2017 19:15:03 GMT )
Sep 26, 2017 19:15 UTC
  • Sojojin Kasar Sin, Suna Gudanar Da Atisaye A Kasar Djibouti:

Kwamandan sojan China a kasar Djibouti Liang Yang ya ce; Sojoji masu yawa ne suke atisayen domin samun karin kwarewar aiki da kuma sarrafa sabbin na'urori.

Liang Yang ya kara da cewa; Wannan shi ne karon farko da sojojin na Sin za su fita daga sansaninsu na Djibouti domin yin atisaye da albarusai masu rai.

Kasar Chana ta bude sansanin soja na farko a kasar Djbouti a cikin watan Augusta, da zummar kai dauki ga sojojin ruwan China da suke a wajen kasarsu.

A 2008 ne dai kasar China ta tura sojojin ruwanta zuwa gabar ruwan Somaliya domin fada da masu fashi a doron ruwa.