-
Wasu Sun Rasa Rayukansu Sakamakon Rikicin Da Ya Barke A Kongo
Dec 20, 2016 18:23Rahotanni daga Jamhuriyar Demokradiyar Congo na cewa alal akalla wasu fararen hula su biyu sun rasa rayukansu kana wasu sun sami raunuka sakamakon bude wuta da sojoji suka yi kan mutanen da suke ci gaba da zanga-zangar nuna adawa ga shugaba Joseph Kabila na kasar.
-
Shugaba Joseph Kabila Ya Sanar Da Dage Zaben Shugaban Kasar "Don Kara Shiri"
Oct 05, 2016 10:59Shugaban Jamhuriyar Dimokradiyar Kongo, Joseph Kabila ya sanar da dage zaben shugaban kasar har zuwa watan Disamba na shekara ta 2018, don ba wa hukumar zaben kasar damar kammala shirye shiryen da suka kamata ta yi a cewarsa.
-
Congo : Hukumar Zabe Na Son A Jinkirta Zabubuka
Oct 02, 2016 17:00Hukumar zabe mai zamen kan ta a Jamhuriya demokuradiyyar Congo na son a jinkirta zabubukan kasar har zuwa watan Nowamba na shekara 2017 mai zuwa.
-
Shugaba Kabila Ya Gana Da Paparoma Kan Rikicin Siyasar Kasr
Sep 27, 2016 05:51Shugaban kasar Demokradiyyar Kongo Joseph Kabila ya gana da shugaban mabiya darikar katolika ta duniya Paparoma Francis na 2 a fadarsa da ke Vatican na kasar Italiya don tattaunawa da shi dangane da rikicin siyasa da ya kunno kai a kasar.
-
Congo : An Ci Zarafin Jama'a Gabannin Zabe
Sep 25, 2016 05:45Wani rahoto da hadin gwiwar wasu kungiyoyin siyasa da na fararen hula suka fitar a kasar congo, ya nuna cewa akalla mutane dari ne aka ci zarafinsu gabanin zaben raba gardama da kuma na shugaban kasa da Denis Sassou Nguesso ya lashe.
-
Ana ci gaba da sukan kungiyoyin kasa da kasa kan shirun da suka yi game da rikicin Jumhoriyar Kwango
Sep 23, 2016 05:50'Yan adawar Gwamnatin Demokaradiyar Kwango sun yi kakkausar suka kan kungiyoyin kasa da kasa kan yadda suka yi shuru dangane yadda Gwamnatin Kwango ke ci gaba da muzgunawa 'yan adawa a kasar
-
MDD Ta Nuna Damuwa Kan Rikicin Da Ke Gudana A Demokradiyyar Kongo
Sep 20, 2016 09:21Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya bukaci jami'an tsaron kasar Demokradiyyar Kongo da su kai zuciyarsu nesa a mu'amalarsu da masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin kasar, biyo bayan rikicin da ya barke a kasar da yayi sanadiyyar mutuwar wani adadi mai yawa na mutane
-
Hukumar Zaben Kongo Ta Kai Karar Babbar Kotun Kasar Saboda Jinkirta Zabe
Sep 18, 2016 11:10Hukumar zaben kasar Demokradiyyar Kongo ta kai karar Kotun Kundin Tsarin Mulkin kasar tana mai bukatar jinkirta gudanar da zaben shugaban kasar lamarin da kotun ta ce zai haifar da gagarumin rikici na siyasa kuma mai hatsarin gaske ga kasar.
-
An kashe 'yan tawaye da dama a gabashin Kwango
Sep 08, 2016 10:50Sojojin Demokradiyar Kwango sun sanar da kashe 'yan tawaye da dama a gabashin kasar
-
'Yan sanda sun buda wata ga masu zanga-zanga a Dimokaradiyar Kwango
Aug 17, 2016 18:14Majiyar Labaran kasar Kwango sun sanar da mutuwa tare da jikkatar wasu mahalarta zanga-zanga bayan da jami'an 'yan sanda suka bude musu wuta