Hukumar Zaben Kongo Ta Kai Karar Babbar Kotun Kasar Saboda Jinkirta Zabe
(last modified Sun, 18 Sep 2016 11:10:01 GMT )
Sep 18, 2016 11:10 UTC
  • Hukumar Zaben Kongo Ta Kai Karar Babbar Kotun Kasar Saboda Jinkirta Zabe

Hukumar zaben kasar Demokradiyyar Kongo ta kai karar Kotun Kundin Tsarin Mulkin kasar tana mai bukatar jinkirta gudanar da zaben shugaban kasar lamarin da kotun ta ce zai haifar da gagarumin rikici na siyasa kuma mai hatsarin gaske ga kasar.

Shugaban hukumar zaben (CENI) Corneille Nangaa ne ya sanar da hakan inda ya ce a halin yanzu dai hukumar tana fuskantar matsala ainun dangane da batun gudanar da zaben wanda a halin yanzu take gudanar da sake dubin rajistar masu kada kuri'a don haka ta bukaci a jinkirta lokacin zaben, hakan ne ya sanya ta kai kara babbar kotun kasar.

Wa'adin mulkin shugaba Joseph Kabila na kasar dai zai kare ne a watan Disamba mai zuwa sannan kuma bisa kundin tsarin mulkin kasar ba shi da damar sake tsayawa takarar. To sai dai hukumar zaben ta ce sake duba rajistar 'yan takarar zai kai watan Yulin shekara mai zuwa.

'Yan adawan dai suna zargin Kabila wanda ya hau mulkin kasar a shekara ta 2001 bayan kashe mahaifinsa da kokari wajen tsawaita lokacin zaben don samun damar ci gaba da mulki.