MDD Ta Nuna Damuwa Kan Rikicin Da Ke Gudana A Demokradiyyar Kongo
(last modified Tue, 20 Sep 2016 09:21:41 GMT )
Sep 20, 2016 09:21 UTC
  • MDD Ta Nuna Damuwa Kan Rikicin Da Ke Gudana A Demokradiyyar Kongo

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya bukaci jami'an tsaron kasar Demokradiyyar Kongo da su kai zuciyarsu nesa a mu'amalarsu da masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin kasar, biyo bayan rikicin da ya barke a kasar da yayi sanadiyyar mutuwar wani adadi mai yawa na mutane

Mr. Ban Ki Moon, ta bakin kakakinsa Stéphane Dujarric yayi Allah wadai da rikicin da ya barken wanda ya zuwa yanzu yayi sanadiyyar mutuwar mutane 17 ciki kuwa har da wasu 'yan sanda guda uku a babban birnin kasar Kinshasa, don haka sai ya kirayi jami'an tsaron da su nuna dattako da kuma kai zuciya nesa a kokarin da suke yi na tabbatar da doka da oda.

Rahotanni daga kasar sun ce akalla mutane 17 ne suka mutu a zanga-zangar da 'yan adawa suka shirya da nufin tilasta wa Shugaba Joseph Kabila na kasar yin murabus inda 'yan sandan suka bude wa masu zanga-zangar wuta.

Zanga-zangar dai ta biyo bayan sanarwa da hukumar zaben kasar ta yi ne na cewa ba zai yi a gudanar da zaben shugaban kasar a lokacin da aka tsara gudanarwa a watan Nuwamba mai kamawa ba saboda har ya zuwa yanzu ba ta gama tantance rajistar masu kada kuri'ar ba, lamarin da 'yan adawan suka fassara shi da cewa wani kokari ne kawai na tsawaita wa'adin mulkin shugaba Kabilan wanda ya kamata ya sauka daga karagar mulkin kasar a watan Disamba mai kamawa.