Pars Today
Tsohon Firai Ministan kasar Tunisia ya bayyana cewa gwamnatin kasar Hadaddiyar daular larabawa tana da hannu a kokarin gurgunta demokradiyar kasar Tunisiya.
Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe ya amince da murabus din Pira minista Selom Komi Klassou
Fira ministan Rasha ya gargadi kasar Amurka kan sake kakaba takunkumi kan kasarsa da cewa: Kakaba takunkumin yana matsayin shelanta yakin kasuwanci ne a tsakanin kasashen biyu.
Fira ministan kasar Tunusiya ya bayyana rashin amincewarsa da bukatar shugaban kasar ta neman ya yi murabus daga kan mukaminsa.
Firayi ministan kasar Madagaska, Olivier Mahafaly, ya sanar da yin murabus dinsa don girmama umurnin da kotu ta bayar na kafa gwamnatin hadin kan kasa a kasar da nufin kawo karshen rikicin siyasa da ya kunno kai a kasar.
Bayan matakin da kotun tsarin milkin kasar Gabon ta dauka na kawo karshen Majalisar dokokin kasar, gwamnati ta gabatarwa Shugaban kasar murabus dinta
Kotun tsarin mulki ta kasar Gabon ta ba da umurnin firayi ministan da yayi murabus daga mukaminsa sannan kuma a rusa karamar majalisar kasar bayan da aka jinkirta zaban 'yan majalisar da ya kamata a gabatar a makon da ya wuce.
Sabon firayi ministan kasar Habasha (Ethiopia), Abiy Ahmed, ya sanar da aniyarsa ta yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar da nufin kayyade wa'adin mulkin firayi minista a kasar zuwa wa'adi biyu kacal.
Shugaban kasar Romaniya Klaus Iohannis ya bukaci firayi ministan kasar Viorica Dancila da ta yi murabus daga mukaminta saboda ziyarar sirri da ta kai haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma batun mayar da ofishin jakadancin kasar zuwa birnin Qudus.
Firayi ministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn ya yi murabus daga kan mukaminsa a yau Alhamis, kamar yadda babbar tashar talabijin din gwamnatin kasar ta sanar.