Fira Ministan Tunusiya Ya Bayyana Rashin Amincewarsa Da Bukatar Yin Murabus
(last modified Wed, 25 Jul 2018 19:30:52 GMT )
Jul 25, 2018 19:30 UTC
  • Fira Ministan Tunusiya Ya Bayyana Rashin Amincewarsa Da Bukatar Yin Murabus

Fira ministan kasar Tunusiya ya bayyana rashin amincewarsa da bukatar shugaban kasar ta neman ya yi murabus daga kan mukaminsa.

A martanin da ya maida dangane da bukatar da shugaban kasar Tunusiya Beji Qa'id Essebsi ya gabatar masa na neman yin murabus daga kan mukaminsa dangane da matsalar tabarbarewar tattalin arzikin kasar: Fira minista Youssef Shahed ya bayyana cewa: Canjin gwamnati a Tunusiya a wannan lokaci zai kara wurga harkar tattalin arzikin kasar cikin mawuyacin hali tare da raunana dogaron da abokan huddar Tunusiya suke yi da kasar.

Fira minista Youssef Shahed ya kara da cewa: Gwamnatinsa tana iyaka kokarinta na ganin Tunusiya ta fice daga wannan mummunan kangi da ta shiga, kamar yadda tafi fifita bukatar sake komawa ga majalisar dokokin kasar domin neman amincewarta kan ci gaba da jan ragamar shugabancin kasar.

Tun a farkon wannan wata na Yuli ne shugaban kasar Tunusiya Beji Qa'id Essebsi ya bukaci fira minista Youssef Shahed da ya yi murabus daga kan mukaminsa na fira minista matukar ba zai iya shawo kan matsalar dambaruwar siyasa da na tattalin arziki da kasar ta tsunduma ciki ba.