Pars Today
Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani ya bayyana cewa bai da wani shiri na ganawa da shugaban kasar Amurka a taron MDD na shekara shekara karo na 73.
Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewar Amurka tare da daukin wasu kananan kasashe 'yan amshin shatanta suna kokari ne wajen haifar da yanayin rashin tsaro a Iran, to amma Jamhuriyar Musulunci a shirye take ta tinkare su.
Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani ya kama hanyar birnin NewYork na kasar Amurka don halarttar taron shekara shekara na majalisar dinkin duniya karo na 73.
Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewar a halin yanzu Iran ba ta kiyayya da wata kasa in ban da Amurka, haramtacciyar kasar Isra'ila da 'yan amshin shatansu, don haka sai ya ce: Al'ummar Iran ta hanyar hadin kai da aiki tare za su yi nasara kan makiyansu.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a yau ya tuntubi shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ta wayar tarho, inda suka tattauna kan batutuwa daban-daban da suka shafi alaka tsakanin Faransa da Iran da kuma batun yarjejeniyar nukiliya.
Shugaban kasar Iran ya aike da sakon taya murnar babbar sallah ta lahiya ga shugabannin kasashen musulmi tare da musu fatan alheri.
Shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran ya bayyana cewa Iran ba ta yarda da kasar Amurka ba, haka ma kasashen Turai, China, Canada ba za su yarda da kasar Amurka ba.
A jiya Talata ne shugaban na kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya aike wa takwaransa na Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa sakon taya murna
A wata zantawa da da ya yi a daren jiya da tashar talabijin ta daya ta kasar Iran, shugaban kasar ta Iran Hassan Rauhani ya bayyana takunkumin da Trump ya kakaba wa kasar da cewa, ba zai iya karya lagon Iran ko durkusar da tattalin arzikinta ba.
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Barazana da zarge-zarge marassa tushe da wasu jami'an Amurka suke yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba su bukatar maida martani.