Rauhani Ya Taya Mgangagwa Murnar Zaben Da Aka Yi Masa
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i32671-rauhani_ya_taya_mgangagwa_murnar_zaben_da_aka_yi_masa
A jiya Talata ne shugaban na kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya aike wa takwaransa na Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa sakon taya murna
(last modified 2018-08-22T11:32:13+00:00 )
Aug 08, 2018 07:27 UTC
  • Rauhani Ya Taya Mgangagwa Murnar Zaben Da Aka Yi Masa

A jiya Talata ne shugaban na kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya aike wa takwaransa na Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa sakon taya murna

Wasikar ta kunshi yin kira da a bunkasa alaka a tsakanin kasashen Iran da Zimbabwe tare da cewa; Lokaci ya yi da kasashen biyu za su bunkasa alaka a tsakaninsu, haka nan kuma yin aiki tare a fagen siyasar kasa da kasa.

Rauhani ya yi fatan samun ci gaba ga kasar ta Zimbabwe da al'ummarta

A ranar 30 ga watan Yuli ne aka gudanar da zaben shugaban kasa a Zimbabwe wanda ya bai wa shugaba Emmerson Mgangagwa nasara