Rouhani:Iran Ba Ta Yarda Da Kasar Amurka Ba.
Shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran ya bayyana cewa Iran ba ta yarda da kasar Amurka ba, haka ma kasashen Turai, China, Canada ba za su yarda da kasar Amurka ba.
A yayin da ya gabatar da jawabi a bikin kere-kere na soja da ya gudana a wannan talata, Shugaban jamhoriyar musulinci na Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewa sanatocin Amurka sun samar da kudirin hana shiga yaki da kasar Iran , domin sun cewa Iran din tana karfin da kai mata kari zai janyo kasar asara mai yawa.
Yayin da yake ishara kan karfin kariya da Dakarun tsaron Iran ke da shi, Shugaba Rouhani ya ce Gwamnatinsa za ta yi iya kokarinta wajen daga karfin kariya da tsaro na kasar da nufin kalubalantar duk wani harin wuce gona da iri da za a iya kawo wa kasar.
Shugaba Rouhani ya ce Al'ummar Iran, al'umma dake son zaman lafiya da sauran kasashe, kuma karfafa shirin tsaro a wannan lokaci yana nufin zaman lafiya, domin rashin shiri a wannan zamani yana nufin kirar yaki da kuma baiwa makiya damar kawo wa kasar hari.
A yayin gudanar da wannan biki dai kasar ta Iran ta nuna sabin kere-kare da tayi na bangaren tsaro, cikin harda wani sabon jirgin yaki da aka kera ba tare da wani sashe nasa daya daga aka shigo da shi daga kasashen waje.