Pars Today
Yansanda a kasar Britania sun bayyana cewa sun gano sunan mutumi da ya kai harin kunan bakin wake a safiyar jiya Talata a wani wuri a birnin Manchester.
Kawo yanzu, mutane 22 ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da kusan 60 suka jikkata, sakamakon harin da aka kai a birnin Manchester na kasar Birtaniya.
Rahotanni daga birnin Manchester na kasar Ingila sun bayyanar cewar alal akalla mutane 19 sun rasa rayukansu kana wasu kuma kimanin 50 sun sami raunuka sakamakon fashewar wasu abubuwa a cibiyar raye-raye ta Manchester Arena da ake ganin wani hari ne na ta'addanci.
Daruruwan mata msuulmi ne tare da wasu wadanda ba musulmi ba da suka hada da iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin London, suka taru a kan babbar gadar West Minister da ke tsakiyar birnin London, domin alhinin abin da ya faru.
Musulmin kasar Birtaniya sun yi Allawadai da kakkausar murya dangane da harin ta’addancin da aka kai a birnin London.
Kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS) ta sanar da cewa ita ce ta kai harin ta'addancin da aka kai majalisar dokokin Birtaniya a jiya Laraba, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane biyar ciki har da wanda ya kai harin.
Amurka da Biritaniya sun haramtawa fasinjojin wasu kasashen Larabawa da Turkiyya shiga jirage masu zuwa kasashen da wasu kayayyakin lataroni.
Dubban mutane ne suka gudanar da jerin gwano a birane daban-daban na kasar Birtaniya domin nuna rashin amincewarsu da kiyayyar da ake nuna ma musulmi a kasar da ma sauran kasashen turai.
Ministan harkokin wajen Birtaniya, Boris Johnson, ya ce gwamnatin kasarsa na goyan bayan samar da kasashen Palestinu da Isra'ila, wanda hakan ne kawai mafita ta samar da zamen lafiya a yankin.
Ministan harkokin wajen kasar Biritaniya, Boris Johnson, na ziyara a Banjul fadar gwamnatin Gambia.