Amurka Da Biritaniya Sun Hana Shiga Jirgi Da Kwamfuta
Amurka da Biritaniya sun haramtawa fasinjojin wasu kasashen Larabawa da Turkiyya shiga jirage masu zuwa kasashen da wasu kayayyakin lataroni.
Matakin dai ya shafi kayayyakin wuta irinsu kwamfuta da kyamarori da na'urar bidiyo ta DVD da na'urar yin wasa, amma ban da wayoyi na salula.
Amurka ce dai ta fara sanar da daukan wannan matakin kafin daga bisani Biritaniya ta bi sahu, bisa abunda suka kira kaucewa barazana ta'addanci.
Haramcin wanda zai fara aiki daga ranar Asabar mai zuwa zai shafi jiragen da ke tasowa daga filayen jirgi 10 daga kasashe takwas galibi na Larabawa da suka hada da Saudiyya, Masar, Koweit, Jodan, Hadaddiyar Daular Larabawa, Qatar, Marocco sai kuma Turkiyya.
Kawo yanzu dai babu daya kasa daga cikin jerin wadanan kasashen wadanda galibi kawayen Amurka ne da suka kalubalanci wannan matakin, illah kawai Turkiyya wace ta bukaci Amurka ta sake nazari ko kuma ta sassauta wannan matakin.
Tuni dai kasashen Faransa da Canada suka ce zasu yi nazari akan irin wannan matakin.