An Zanga-Zangar Adawa Da Masu Kin Jinin Musulmi A Birtaniya
Dubban mutane ne suka gudanar da jerin gwano a birane daban-daban na kasar Birtaniya domin nuna rashin amincewarsu da kiyayyar da ake nuna ma musulmi a kasar da ma sauran kasashen turai.
Tashar talabijin ta PressTV ta bayar da rahoton cewa, wannan gangami da zanga da aka gudanar a biranan kasar Birtaniya, ya hada batutuwa da dama da jama'a suke da korafi a kansu.
Daga cikin kuwa har da yadda ake nuna wa musulmi kyama a wasu kasashen turai musamman a Amurka, inda kyamar musulmi ta zama lamari ne a hukumance daga bangaren gwamnatin kasar, da kuma yadda ake nuna tsana ga masu gudun hijira daga kasashen msuulmi da ke fama da matsaloli.
A birnin London ne dai aka gudanar da zanga-zangar mafi girma, inda dubban mutane da suka hada da musulmi da ma wadanda ba musulmi ba suka taru a babban dandalin da ke kusa da majalisar dokokin kasar Birtaniya da ke London, inda suka rika isar da sakonsu ta hanyar rera take da kuma kwalen da suka yi rubutu a kansu.
A cikin lokutan baya-bayan nan dai an samu karuwar kyamar msuulmia wasu daga cikin kasashen turai, sakamakon karuwar kungiyoyin nuna kyama ga addinin muslunci wadanda suke ci gaba da bunkasa harkokinsu da sunan 'yancin fadar albarkacin baki.