Biritaniya : Mutane 22 Suka Mutu A Harin Manchester
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20644-biritaniya_mutane_22_suka_mutu_a_harin_manchester
Kawo yanzu, mutane 22 ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da kusan 60 suka jikkata, sakamakon harin da aka kai a birnin Manchester na kasar Birtaniya.
(last modified 2018-08-22T07:00:09+00:00 )
May 23, 2017 06:49 UTC
  • Biritaniya : Mutane 22 Suka Mutu A Harin Manchester

Kawo yanzu, mutane 22 ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da kusan 60 suka jikkata, sakamakon harin da aka kai a birnin Manchester na kasar Birtaniya.

Hukumomin yankin dai sun dauki al'amarin a matsayin harin ta'addanci.

Bayanai daga kasar sun ce wani mutum ne ya tayar da wani abu mai fashewa a filin a lokacin da ake tsaka da gudanar wasan nishadi.

Filin wasan na Manchester na iya daukar mutane 21,000, kuma kafafen yada labarai sun ruwaito cewa, filin a cike yake a lokacin da lamarin ya auku.