Pars Today
Shugaban kasar Iraki Fuad Masum ya bayyana cewar har ya zuwa yanzu ba a yanke shawarar barin Amurka ta kafa sansanin sojojinta na dindindin a kasar Irakin ba, yana mai cewa gwamnatin Iraki ba za ta taba bari a mai da kasar ta zamanto wani waje da za a kai wa wata kasa ta makwabta hari ba.
Fira ministan gwamnatin kasar Iraki ya sanar da cewa: Sojojin Iraki da dakarun sa-kai na kasar sun kawo karshen duk wani sansanin 'yan ta'adda a duk fadin kasar Iraki.
Jmai'an tsaron kasar Iraki sun bankado wani shirin 'yan ta'addan takfiriyya na kai hari a yankin Anbar da ke arewacin kasar ta Iraki.
Kungiyar ta'addancin nan ta ISIS ta kai hari kan wurin binciken jami'an tsaro tare da kashe mutane 6
Dakarun sa kai na hashadu-sha'abi da jami'an 'yan sandar kasar Iraki sun kadamar da ayukan tsarkake yankunan kudu maso yammacin kasar daga tsirarun 'yan ta'addar ISIS din da suka rage
Majalisar dokokin kasar Iraqi a zamanta na ranar Alhamis da ta gabata daya ga watan Maris Shekara ta 2018 ta amince da wata doka wacce ta bukaci gwamnatin kasar ta fayyace ranar ficewar sojojin kasashen waje daga kasar.
Pira ministan kasar Iraki Haidar Ibadi ya cimma matsaya da Amurkawa akan wajabcin ayyana lokacin ficewarsu daga cikin kasar.
Gwamnatin kasar Iraki ta yi watsi da bukatar da gwamnatin Saudiyya ta gabatar mata na ta mika mata wasu 'yan kasar (Saudiyyan) sama da 400 da ake tsare da su saboda samunsu da laifin aikata ayyukan ta'addanci a kasar Irakin.
Shugaba Michel Aoun, na Labanon, ya gana da takwaransa, Fuad Massum, na Iraki, a Bagadaza a wata ziyara wacce ita ce irinta ta farko da wani shugaban kasar Labanon ya taba kaiwa a wannan kasa.
Kasashen duniya, sun alkawarta samar da dalar Amurka Biliyan talatin, don sake gina kasar Iraki, da yakin da aka shafe tsawon shekara uku ana yi da kungiyar 'yan ta'adda ta (IS) ya daidaita.