Pars Today
Ministan harkokin wajen kasar Kuwaiti ya bayyana cewa; Kawo ya zuwa kudaden da aka yi alkawalin za a bayar domin sake gina Iraki sun kai dalar Amurka biliyan 30
Hukumar abinci da noma ta dunia FAO ta bada rahoton cewa kashi 40% na albarkatun noma na kasar Iraqi sun lalace sanadiyyar yaki da ta'addanci a kasar.
Rundunar Sojan Iraki mai fada da ta'addanci ce ta sanar da gano mabuyar makaman a cikin wurare daban-daban na babban birnin kasar.
Jami'an hukumomin leken asirin kasashen Iran, Iraki, Siriya da Rasha sun gudanar da zaman taro a tsakaninsu a birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki a jiya Lahadi.
Tashin bom a yankin arewacin birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki ya lashe ran mutum guda tare da jikkatan wasu biyu na daban.
Rundinar sojin Turkiyya ta kai hare-haren sama a kan wasu sansanonin mayakan Kurdawa na PKK a arewacin Iraki.
Wata kotu a birnin Bagadaza na Iraki ta yankewa wata 'yar asalin kasar Jamus hukuncin kisa, saboda alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta IS.
Ma'aikatar 'yan gudun hijra ta kasar Iraki ta sanar da komawar 'yan kasar ta kimanin dubu 31 zuwa 'yan kunansu da aka tsarkake daga kasashen Turkiya da Siriya
Haydar Abadi ya ce a ranar 12 ga watan Mayu na wannan shekarar ta 2018 ne za a gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar.
Babban sakataren Majalisar dinkin duniya ya yi Allah wadai da hare-haren ta'addanci guda biyu da aka kai birnin Bagdaza a jiya Litinin.