Iraki: Yarjejeniyar Ficewar Sojojin Amurka
Pira ministan kasar Iraki Haidar Ibadi ya cimma matsaya da Amurkawa akan wajabcin ayyana lokacin ficewarsu daga cikin kasar.
Wani dan majalisar kasar Iraki Jasim Muhammad Ja'afar ya fada a jiya alhamis cewa; PIr ministan kasar Haidar Ibadi ya tattauna da Amukrwa akan fitar da sojojinsu daga Irakin.
Ibadi ya fada wa Amurkawan cewa; Al'ummar Iraki ba su son ganin Amurka ta kafa wani sansani a cikin kasarsu.
Dan Majalisar kasar ta Iraki ya ce; Sai dai duk da haka abu ne mai yiyuwa Amurkan ta kafa sansaninta a yankin Kurdawa wanda gwamnatin tsakiya ba ta ido akai.
A jiya alhamis din, majalisar dokokin Iraki ta amince da dokar tilastawa gwamnati tsaida lokacin da sojojin Amurka za su fice daga kasar.