Pars Today
Jagoran 'yan adawa na Nijar, kana shugaban jam'iyyar Moden Lumana, Hama Amadu, ya rasa mukaminsa na dan majalisar dokoki.
Gwamnatin kasar Demokradiyyar Kongo ta sanar da cewa tsohon mataimakin shugaban kasar, Jean-Pierre Bemba, da kotun duniya mai shari'ar manyan laifuffuka (ICC) ta wanke na iya komawa gida, sai dai ba ta ce ko za a hukunta shi a kasar idan ya dawo ba.
Alkalan kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuffuka ICC sun ba da umurnin a sake tsohon mataimakin shugaban kasar Kongo kana kuma tsohon magudun 'yan tawayen kasar Jean-Pierre Bemba daga inda ake tsare da shi bayan bangaren daukaka kara na kotun ya wanke shi daga zargin aikata laifuffukan yaki da cin zarafin bil'adama da ake masa.
Kotun hukunta manyan laifufuka ta ICC da ke birnin Hague ta wanke tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo kana kuma tsohon madugun 'yan tawayen kasar, Jean-Pierre Bemba, daga tuhumar da aka masa na tafka laifukan yaki da cin zarafin bil'adama.
Wata babbar kotun tarayya a Kaduna, da ke arewacin Nijeriya ta ba da umurnin a tsare tsohon gwamnan jihar Mukhtar Ramalan Yero da wasu mutane uku a gidan yari saboda zargin cin amana da halatta kudin haram.
Wata kotu a kasar Kamaru ta yanke hukunci daurin shekaru 15 a gidan Kaso kan wasu shugabani na yankin dake amfani da turancin inglishi bisa laifin ta'addanci a kasar
Ministan harkokin wajen Palasdinu, Riyad al-Maliki, ya bukaci kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa, data bude binciken gaggawa kan laifukan yaki da wariyar launin fata da ake zargin aikata wa kan Palasdinawa.
Kotun tsarin mulki ta kasar Gabon ta ba da umurnin firayi ministan da yayi murabus daga mukaminsa sannan kuma a rusa karamar majalisar kasar bayan da aka jinkirta zaban 'yan majalisar da ya kamata a gabatar a makon da ya wuce.
Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta sake yin watsi da bukatar bada belin tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo.
A yau Juma'a, tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya gurfana a gaban babbar kotun birnin Durban saboda zargin da ake masa na cin hanci da rashawa kan wani ciniki na makamai da suka kai dala biliyan 2.5 da aka yi tun a shekarun 1990.