Kotu A Kaduna Ta Turo Tsohon Gwamnan Jihar, Yero, Gidan Yari
(last modified Thu, 31 May 2018 15:59:11 GMT )
May 31, 2018 15:59 UTC
  • Kotu A Kaduna Ta Turo Tsohon Gwamnan Jihar, Yero, Gidan Yari

Wata babbar kotun tarayya a Kaduna, da ke arewacin Nijeriya ta ba da umurnin a tsare tsohon gwamnan jihar Mukhtar Ramalan Yero da wasu mutane uku a gidan yari saboda zargin cin amana da halatta kudin haram.

Alkalin kotun mai shari'a, Mohammed Shuaibu, ne ya ba da wannan umurnin a yau din nan bayan da hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da tsohon gwamnan da mukarraban nasa su uku wato tsohon minista Nuhu Way; tsohon sakataren gwamnatin jihar, Hamza Ishaq da kuma tsohon shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Haruna Gaya. a gaban kotun saboda zargin da suka hada da halatta kudin haram da hada baki wajen aikata babban laifi da karkatar da dukiyar al'umma da kuma cin amana na kudade da suka kai Naira miliyan 700 a lokacin zaben shekara ta 2015.

Mutanen da ake zargin dai sun musanta wannan zargi da ake musu, don haka alkalin kotun ya ba da umurnin a ci gaba da tsare su a gidan yari har zuwa ranar 6 ga watan Yuni mai kamawa don yanken hukunci kan bukatar beli da tsohon gwamnan ya gabatar.

Hakan yana zuwa ne bayan da a jiya Laraba hukumar EFCC din ta sami nasara a shari'ar da take yi da tsohon gwamnan jihar Jolly Nyame inda wata kotu a Abuja ta daure shi shekaru 14 a gidan maza saboda laifin cin dukiyar gwamnati.