Pars Today
Haydar Abadi ya ce; aikewa da sojojin zuwa Karkuk da Kurdawa suke yi tsokana ce mai hatsari.
Kasashen Turkiyya Da Iran sun karfafa matakan ayyukan soji a wani mataki na tsaron iyakokinsu.
Kasashen duniya na ci gaba da goyan bayan dunkulewar Iraki a matsayin kasa daya, bayan da Kurdawan aksar suka kada kuri'ar raba gardama, a wani yunkuri na neman 'yancin kan yankin Kurdistan.
Sakamakon zaman dar-dar da ake ciki a Kurdistan na Iraki bayan zaben raba gardama da aka gudanar 'yan kasashen waje na ficewa daga yankin.
Manyan hafsoshin sojojin kasar Iran da Iraki sun yi wata ganawa ta musamman a nan birnin Tehran don tattauna batun zaben raba gardamar da aka gudanar a yankin Kurdawan aksar Iraki da nufin balle yankin daga kasar Iraki.
Amurka ta sanar da cewa ta ji takaici sosai akan zaben raba gardama ballewar yankin Kurdawan Iraki, tare da cewa hakan zai kara dagula al'amuran tsaro da wahalhalu a yankin.
Shugaban Majalisar dokokin kasar Iraki ya tabbatar da cewa zaben raga gardamar da za a yi na ballewar yankin kurdawa daga kasar iraki ba zai yi wani tasiri a dokance ba.
Shugaban yankin Kurdawan Iraki, Massoud Barzani, ya yi kira ga Kurdawa dasu fito zaben raba gardama da za'a kada kuri'arsa a gobe Litini.
Gwamantin Iran ta sanar da dakatar da dukkan zurga-zurga jiragan sama zuwa yankin Kurdistan na Iraki, a yayin da ake gaf da jefa kuri'ar raba gardama kan ballewar yankin na Kurdawa.
kurdawa Da Shirin Ballewa Daga Iraki