Iran Ta Dakatar Da Zirga-Zirga Jiragan Sama Zuwa Kurdistan Na Iraki
Gwamantin Iran ta sanar da dakatar da dukkan zurga-zurga jiragan sama zuwa yankin Kurdistan na Iraki, a yayin da ake gaf da jefa kuri'ar raba gardama kan ballewar yankin na Kurdawa.
An dai dau wannan matakin ne bisa bukatar gwamnatin Bagdad, a cewar kakakin majalisar koli ta tsaron kasar ta Iran, Keyvan Kosravi, kana kuma a cewarsa hakan ya biyo bayan nacewar jagororin Kurdawan akan shirin zaben raba gardama wanda duk yunkurin Iran na ganin an samu mafita ya cutura.
Kamfanonin jiragen saman Iran wanda suka hada da Mahan Air da Caspian Air na gudanar da zurga zurga a ko wannan mako zuwa Kurdistan tun daga birane da dama na Iran.
Iran dai wacce ta kunshi Kurdawa kimanin Miliyan shida daga cikin miliyan tamanin na al'ummar kasar na adawa da shirin ballewa na Kurdawan wanda ta ce zai iya hadassa wani sabon rikici a yankin.
Kasashen Tukiyya Amurka da ma kasashen Turai na adawa da shirin zaben ballewa na Kurdiwan Iraki.
Kawo yanzu dai mahukuntan yahudawan mamaya na Isra'ila ne kawai suka nuna karara goyan bayansu kan ballewar kurdawan na Iraki.
A ranar hudu ga watan gobe ne ake sa ran shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya zai kawo wata ziyara a nan Teheran domin tattauna halin da ake ciki a yankin Kurdistan na Iraki.