Sep 11, 2017 18:27 UTC
  •  Kurdawa Da Shirin Ballewa Daga Iraki              ( 3)

kurdawa Da Shirin Ballewa Daga Iraki

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan fitowar ta shirin mu leka mu gani. Shiri ne dai wanda mu ka saba kawo muku batutuwan da su ka shafi fuskoki daban-daban na rayuwa.

To har yanzu masu saurare muna a tare da ku a cikin batun kurdawa da shirinsu na kada kuri'ar raba gardama akan makomar yanki.

Kawo ya zuwa yanzu kuwa mun gabatar muku da shiri biyu, yau kuma za su ci gaba da na uku.

Da fatan za ku kasance a tare da mu domin a ji yadda ci gaban shirin zai kasance.                      

Kiran ballewa daga Iraki da Barzani yake yi yana shan suka daga cikin kasar da kuma yankin. Suka ta farko da ake yi yi masa shi ne cewa ya nada kansa mai Magana da dukkanin yanwun kurdawan yankin gabas ta tsakiya. Hakan yana nufin shiga shugula cikin karkokin wasu kasashe kamar Iran da Turkiya da Syria.

Wata sukar da ake yi masa ita ce idan ma da gaske ne cewa yana Magana ne da yawun sauran kurdawa, to abinda yake son cimmawa ba daidai ba ne. Domin kuwa a cikin kasar Iraki, Kurdawan sun sami dukkanin abinda su ke so. Kuma a karkasyhin tsarin mulkin kasar ta IRaki, suna da hakkin kwarya-kwaryar cin gashin kai, da tsarin mulki na yankinsu,. Amma batun yin kuri'ar raba gardama domin ballewa yana cin karo da tsarin mulkin kasar.

Suka ta uku da ake yi wa kurdawan masu son ballewa a karkashin Barizani ita ce, batun Yugoslavia da cheslovakia da ya kafa misali da su, wasu aubuwa da suka shafi harkokin cikin gidan kasashen da basu shafi wasu kasashe ba. Abin nufi anan shi ne, rabewar kasar Yogoslavia da Cheslovakia ya shafi al'ummun wadannan kasashen ne kawai, bai da wani tasiri ga wasu kasashen ta fuskar tsaro.

 Su kuwa Kurdawa suna a cikin kasashen 4 ne da sune Turkiya, Iran, Iraki, da Syria. Idan kurdawan na Iraki suka balle to hakan zai yi tasiri ta fuskar tsaro akan sauran kasashen. Don haka ba kasar Iraki ce kadai take adawa da ballewar kurdawan ba, hadda kasashen Irak da Turkiya da Syria.

Me ya sa kurdawan su ke son ballewa duk da matsayi na musamman da suke da shi a karkashin tsarin mulkin Iraki da kuma rabon dukiyar da ake yi da su daidai wadaida.?

Mene ne manufar yin kuri'ar raba gardama?

  1. Dalili na cikin gida:

 

A cikin yankin Kurdistan an kai bango dangane da batutuwan siyasa. Daga cikin batutuwan da suka ki ci su cinye a yankin sun kunshi tsarin mulki da majalisar dokoki da shugabanci," tsawon lokaci kowane daya daga cikin wannan abubuwan uku ya kai bango.

Abisa yadda aka tsara a 2009 ne za a yi kuri'ar raba gardama a yankin, dangane da tsarin mulkin yanki, sai dai shekaru 8 sun shude hakan ba ta faru ba. Kuma a cikin shekarar 2013 ne aka yi zabe na karshe na majalisar dokoki, sai dai kawo ya zuwa yanzu babu wani yaki na abo a gani da su ka gudar. An jingine aiki da suke yi a yankin baki daya.

Shi kanshi shugabanci a yankin na kurdawa ya kai bango. A 2013 ne zangon shugabancin Barzani ya kare, amma Majalisar yankin kafin ta daina aiki, ta kara tsawon wa'adin shugabancin Barzani na shekaru biyu, duk da cewa wasu jam'iyyun siyasar kasar sun nuna kin amincewarsu.

Sai dai bayan gushewar shekaru biyun da aka kara masa, bai sauka ba, ya sake kara wa kansa wasu shekaru biyu.

Wannan matsalolin guda uku da yankin yake fama da su, sun  jefa yankin cikin halin kiki-kaka.

Bugu da kari al'ummar yankin suna cikin yin koke akan yaduwar cin hanci da rashawa. Suna sukar Barzani da jam'iyyarsa da wadanda su ke zagaye da shi da wasa da dukiyar al'umma.

Don haka a fili yake cewa, bijiro da batun kuri'ar raba gardama a cikin yankin kokari ne na rufe matsalolin da ake fama da su, da suka kai yankin ga bango.

Shorash, Haji, wanda shi ne kakakin yunkurin kawo sauyi a yankin yana fadin cewa:

"  Idan jam'iyyar Kudistan Democrati Party ba ta karbi sharadinmu na jingine maganar kuri'ar raba gardama ba, to ba za mu shiga tattaunawar bangare biyu da su ba. Kuma yin kuri'ar raba gardama a 25 ga wata mai zuwa, tarbar aradu ne da kai da wasa da makomar yankin kurdawa."

A sabili da haka, batun yin kuri'ar raba gardama, ya shafi siyasar cikin gida ne kawai. Mas'udu Barzani da jam'iyyarsa suna son sayen lokaci ne da kuma kaucewa matsin lambar da su ke fuskanta a cikin gida. Kuma yana son mutanen yankin da suke matsa masa lamba su maida hankali kan Bagadaza sannan kuma yana son gwamnatin tarayyar din ta kara masa kasafin kudi.

 

 

Tags