Nov 02, 2017 11:53 UTC
  • Iraki: Gwamnatin Bagadaza Ta Zargi Arbil Da Rashin Aiki Da Yarjejeniyar Tsaro

Sojojin Kasar ta Iraki sun ja kunnen yankin na Kurdawa akan idan ba su yi aiki da yarjejeniyar ba ta tabbatar da tsaro a iyakoki, to za su shiga da kansu.

Tashar telbijin din Sumariyyah ta Iraki  ta ambato sojojin suna ci gaba da cewa; Za su sake bai wa Arbil wata dama domin aiki da yarjejeniyar gabanin su shiga da kansu domin tabbatar da tsaro.

Bayani ya kunshi cewa; Bisa nauyin da pira minista kuma kwamandan sojojin kasar Iraki ya  dauka, ya aike da kwararrun sojoji da suka yi taruka da dama da jami'an tsaron Arbil, domin kaucewa zubar da jini tare da ayyana musu lokaci domin tabbatar da tsaro, amma har ranar 31 ga watan Oktoba ba su yi ba.

Sojojin na Iraki dai suna shirin kafa cibiyoyi ne a iyakokin yankin na kurdawa da mashigarsa da iyakokin waje.

Tags