Pars Today
Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Na'im Kasim ya bayyana Amurka a matsayin babban karfen kafa ga duk wani yunkurin samar da sulhu da zaman lafiya a Syria.
Shugaban kasar Lebanon Micheal Aun ne ya bayyana haka a yau litinin da yake ganawa da wakilin Majalisar Dinkin Duniya a birnin Beirut.
Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan nasrullah ya bayyana cewa; Amurka da 'yan korenta suna hankoron ganin bayan duk wani yunkuri wanda zai hana su cimma bakaken manufofinsu a kan al'ummomin yankin gabas ta tsakiya.
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lobnon ya yi ishara kan kashin da Amirka da kawanta suke sha a yankin\, inda ya ce a yau, lokaci ya yi na raba abinda muka girba, kuma mahiman nasarorin da muka samu shi ne goyon bayan gwagwarmaya a yankin.
Shugaba Michel Aoun, na Labanon, ya gana da takwaransa, Fuad Massum, na Iraki, a Bagadaza a wata ziyara wacce ita ce irinta ta farko da wani shugaban kasar Labanon ya taba kaiwa a wannan kasa.
Babban kwamandan sojojin kasar Labanon, Janar Joseph Aoun, ya ja kunnen haramtacciyar kasar Isra'ila da cewa lalle za a mayar mata da martani ta dukkanin hanyar da ta sawwaka matukar ta kawo wa kasar Labanon din hari.
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya kara jaddada cewa Hizbullah tana kan wasiyan da shuwagabannin shahidan kungiyar suka bar masu.
Ministan ma'aikatar ilimi a Haramtacciyar kasar Isra'ila ya kirayi gwamnatin yahudawan da ta yi taka tsantsan wajen kauce wa duk wani abin da ka iya jawo barkewar wani sabon yaki a tsakaninsu da Lebanon.
A ranar 29 ga watan Janairun da ya gabata ne wata fitana ta kunno kai a harkokin siyasar Kasar Lebanon wacce ta kai ga cacar baki tsakanin magoya bayan shugaban kasar Michel Aoun da kuma na Kakakin majalisar dokokin kasar Nabi Berri.
Sojojin na Lebanon sun fara kai farmaki akan yankin Babul-Tubbanah da ke garin Tripoli a arewacin kasar.